
Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa, Yana goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce a shekarar 2027.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV.
Yace dalilinsa shine yana son kamar yanda Arewa ta yi shekaru 8 akan mulki, itama kudu ta kammala shekaru 8.
Yace yana mamakin dan Arewa ya rika cewa an cuci Arewa a tsarin karba-karba na mulki a Najeriya.