
Tauraruwar fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa ta mutu.
Samha a sanarwar data fitar ta shafinta tace ta fito ta sanar da mutanene cewa, tana samun sauki kuma ba kamar yanda wasu ke yadawa ba cewa wai ta mutu, tace tana nan da ranta.
Ta yi godiya da ‘yan uwanta da abokan sana’arta da masoya da suka nuna damuwa game da abinda ya sameta.