Wednesday, November 12
Shadow

Kada ma ka yi tunanin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 dan ba zaka ci ba>>Wata Kungiyar Yarbawa ta gayawa shugaba Tinubu

Wata Kungiyar Yarbawa me suna Ìgbìnmó Májékóbájé Ilé-Yorùbá ta bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gaza a fannin inganta tattalin arziki da samar da tsaro.

Kungiyar a sanarwar data fita daga bakin shugaban ta, Olusola Badero wanda me magana da yawunta, Princess Balogun ya fitar.

Yace Talauci musamman a yankin Yarbawa ya karu hakanan matsalar tsaro ta karu.

Ya kawo misalin cewa kwanannan aka sace wasu manoma a yankin inda sai da danginsu suka tara kudi sannan aka sakesu.

Yace Tinubu ya kasa cika Alkawuran da ya dauka, dan haka yace Aso Rock ba gidan gado bane, kada ma Tinubu yayi tunanin tsayawa takara a 2027 dan ba ci zai yi ba.

Karanta Wannan  Bidiyo: RIKICIN APC: Lamarin Fa Ya Wuce Tunani, Domin An Nuno Gwamna Zulum A Fusace Ana Rarrashinsa, An Kuma Hango Wani Ya Daga Kujera Ya Maka Wani, Inda Kuma Aka Kyallaro Wani Ya Tube Malam-Malam Yana Kai Naushi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *