Friday, December 5
Shadow

Ina tare da jam’iyyar ADC amma bazan fita daga PDP ba>> InjiSule Lamido

Ba zan bar PDP ba amma ina maraba da haɗakar ƴan adawa don ƙwatar mulki a 2027 – Sule Lamido.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce a shirye yake ya mara wa kowacce haɗaka ta ƴan adawa don kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Lamido ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Vanguard a Abuja a jiya Laraba.

Lamido ya ce ko da ya ke yana goyon bayan haɗewar jam’iyyun adawa ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bisa jagorancin Sanata David Mark, ba zai fice daga jam’iyyarsa ta PDP, wadda ya ce da shi aka kafa ta ba

Ya ce ba daidai ba ne a watsar da PDP saboda waɗanda ya kira “marasa godiya” da ke ƙoƙarin lalata jam’iyyar.

Karanta Wannan  Labarin cewa tsohuwar matar Ahmad XM, Safiya zata auri Hambali ba gaskiya bane

“Eh a shirye na ke da duk wani yunkuri na kifar da APC don a ceci Najeriya. Zan mara wa duk wanda ke da wannan buri. Zan yi kamfe tare da su. Amma mu PDP ita ce jam’iyya ta. Ko da ya ke tana fuskantar rikici, zan zauna in yi gwagwarmaya don ceto ta.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *