
An sami wani marar tsoron Allah yayi amfani da AI ya cirewa Rahama Saidu kaya daga jikinta aka ganta Tùmbùr.
Saidai wannan hoto da yayi na karkirane, ba Rahama ce ta saka wannan hoton ba.
Abokin Rahama, Baba Sadik Yayi Martani kan wannan lamari amar haka:
“ILLAR (AI) WATO ARTIFICIAL INTELLIGENCE BARAZANE SOSAI GA MUTANE
Illar AI a wannan zamani ba ƙaramin abu bace Fasaha ce mai kyau kuma mai amfani sosai, amma tambayar ita ce yadda muke amfani da ita. Mu ’yan Najeriya, Allah Ya ba mu basira da ilimi na musamman; gaskiya ne, yan Najeriya unique ne, kuma muna da hazaka sosai.
Amma abin takaici, sau da yawa muna karkatar da wannan ilimi zuwa shirme da shashanci, maimakon muyi amfani da shi wajen alheri da gina al’umma.
Yanzu wanda ya ƙirƙiri irin waɗannan abubuwa yana ganin kamar abin burgewa ne, amma ya kamata ya sani cewa Allah na kallon komai, kuma kowa zai tsaya a gabansa a ranar hisabi.
Wallahi ya dace mu rika amfani da tunaninmu da fasaharmu inda ya dace, ba wajen ɓata suna, mutunci, ko cutar da wasu ba.
Ku tuna cewa iyayenmu basu san irin wannan fasaha ba, sau da yawa sai an ɗauki lokaci mai tsawo kafin su gane cewa abin da suka gani ba gaskiya ba ne. Na shaida hakan da kaina lokacin da mama ta taga wani abu makamancin haka, ta yi matuƙar mamaki, sai da na yi mata bayani sosai kafin ta fahimci cewa kirkira ce, ba gaskiya ba. Idan ba mu yi hattara ba, za mu iya jefa iyayenmu da al’umma cikin ruɗani da tashin hankali ba tare da sun sani ba.
Yau ana yin wannan abu ga mata, gobe ana iya yi wa malamai masu daraja, jibi ’yan siyasa, sannan daga baya kowa zai iya zama abin hari. Mutunci da daraja su ne ginshiƙan zaman lafiya, kuma ya wajaba mu kiyaye su.
Don Allah, mu gyara.
Mu yi amfani da AI wajen ilimi, cigaba, da kirkire-kirkire na alheri, ba wajen shirme, ƙarya, da ɓata sunan jama’a ba. Gaskiya ita ce ginshiƙin mutunci, kuma duk wanda ya lalata ta, ya lalata kansa da al’umma baki ɗaya.
BabaSadiq Bs Media Concept”