
Kungiyar da ta kaiwa tawagar Brigadier General Muhammad Uba harin kwantan bauna, ta kamashi kuma ta kashe, watau ÌŚWÀP ta saki hoton gawarsa.
Hakanan ta saki Hoton Screenshot na WhatsApp Chat da yayi da sojoji inda yake gaya musu inda yake dan su zo su ceceshi, an ga inda yake cewa, Su yi Sauri Chajin wayarsa ya kusa daukewa.
Lamarin akwai sosa Zuciya sosai.
Wani abin karin bacin rai shine yanda aka ga suna ta dariya suna mai shagube.
A hoton an ga Jini yana kwarara daga kunnensa sannan a kafarsa akwai harbin Bindiga.


