Friday, June 26
Shadow

An dakatar da bayar da làsìsìn Màkàmì irin su Bhìndìghà ga ‘yan Najeriya dan su yi amfani da ita wajan kare kansu>>Inji Hukumar ‘yansandan Najeriya

Hukumar ‘yansandan Najeriya ta tabbatar da cewa, dokar hana bayar da lasisin Mallakar Bindiga a Najeriya dan kariyar kai har yanzu tana aiki.

Me magana da yawun hukumar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka a wani martani da yayi game da ikirarin da wani yayi cewa ya mallaki Bindigar AK47.

Benjamin yace a doka ko da ana bada lasisi, Bindigar AK47 bata cikin wadda aka amince farar hula su rike.

Yace amma a yanzu har yanzu ba’a dage dokar data hana bayar da lasisin Mallakar Bindiga dan kariyar kai ba.

Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda mutane suka rika tambayar to su tsageran daji ina suka samo nasu Bindigun?

Karanta Wannan  Doka ta bayar da dama idan Gwamnati ta gaza, 'yan Najeriya zasu iya neman taimakon kasashen Duniya game da harkar tsaro>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *