
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya taya matarsa, Titi Abubakar murnar cika shekaru 75 a Duniya.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace yana godiya da hakuri da ta yi da rauninsa. Inda ya jawo hankalin ma’aurata su rika hakuri da juna.
Atiku yace duka iyayensu basu amince ba suka yi aure kuma abokai 2 ne kadai suka halarci wajan daurin aurensu.
Yace amma gashi yau sun cika shekaru fiye da 50 da yin aure.
Atiku ya bayyana hakane a shafin sa na sada zumunta.