Wednesday, January 15
Shadow

Jadawalin wasannin Premier League makon farko

Ranar Juma’a 16 ga watan Agusta

  • Manchester United da Fulham

Ranar Asabar 17 ga watan Agusta

  • Ipswich Town da Liverpool
  • Arsenal da Wolverhampton
  • Everton da Brighton
  • Newcastle United da Southampton
  • Nottingham Forest da Bournemouth
  • West Ham United da Aston Villa

Ranar Lahadi 18 ga watan Agusta

  • Brentford da Crystal Palace
  • Chelsea da Manchester City

Ranar Litinin 19 ga watan Agusta

  • Leicester City da Tottenham

Wasu mahimman batuwan da suka shafi Premier League 2024/25

Manchester City za ta buga wasa biyu daga bakwai kafin Champions League, wadda za ta yi uku a Etihad da Aston Villa da Arsenal da kuma Liverpool.

Wasa mai nisa da za a buga shi ne mil 200 ranar 26 ga watan Disamba da Arsenal za ta ziyarci Newcastle United a St James Par.

Karanta Wannan  Karanta Jadawalin Daraktoci 14 da CBN suka kora daga aiki

Makon karshe da za a fafata don lashe FA Cup, shi ne Asabar 17 ga watan Mayu, ranar ba za a kara a Premier League ba.

A mako na uku a kakar da za a fara Aston Villa za ta je gidan Tottenham, yayin da Liverpool za ta karbi bakuncin Chelsea a Anfield.

A wasan mako na hudu kuwa Manchester City za ta je gidan Tottenham daga nan ta kece raini da Liverpool.

Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool ikafin hutun kalandar Fifa a Satumba, Arsenal ta ziyarci Tottenham ana kammala hutun.

Everton za ta buga wasan karshe a Goodison Park – daga nan ta koma Bramley-Moore Dock – za ta fara karawa da Southampton ranar Lahadi 18 ga watan Mayu a makon da za a buga wasan karshe a FA Cup.

Karanta Wannan  Za'a gyara titunan zuwa dakin dafa abinci na shugaban kasa Tinubu, da wanda jiragen samansa ke bi da wanda ake bi dan kai masa ziyara akan Naira Biliyan 9.8

Yaushe za a fara wasannin Premier League 2024/25?

Za a fara Premier League kakar 2024-25 ranar Juma’a 16 ga watan Agusta a karkare ranar Lahadi 25 ga watan Mayun 2025 da yin wasa 10 rana daya a lokaci tare.

Za a yi mako 33 da yin karawa a tsakiyar mako karo hudu da daya a lokacin Kirsimeti, wato ranar 26 ga watan Disamba.

Za a yi hutun Fifa da ta kan bayar cikin watan Satumba da Nuwamba da kuma watan Maris, yayin da za a buga wasan zagaye na uku a FA Cup a makon nin Janairu.

Domin samun buga karawar tsakiyar makon Agusta, babu hutu a lokacin hunturu, yayin da ba za a maimaita wasa ba kwana daya kafin Kirsimeti da aka yi tsakanin Wolves da Chelsea ba a kakar da ta wuce, karon farko tun 1995.

Karanta Wannan  Ba za mu taɓa yin sulhu da 'yan bindiga ba - Gwamnan Zamfara

An sanar da kungiyoyin da za su buga Premier League cewar ba wadda za ta buga wasa biyu a jere kasa da awa 60 a tsakanin Kirsimerti da sabuwar shekara.

Ukun da suka samu shiga Premier League da wadanda suka yi ban kwana

Kungiyoyin ukun da suka hauro zuwa Premier League, sun hada da Leicester City, wadda ta lashe Championship da kuma Ipswich ta biyu.

Ta ukun ita ce Southampton, wadda ta yi nasara a kan Leeds United a karawar cike gurbi.

Wadanda suka yi ban kwana da wasannin da aka kammala sun hada da Luton Town da Burnley da kuma Sheffield United.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *