Wednesday, January 8
Shadow

Jamb ta samu kudin shiga Biliyan 22.9 inda ta baiwa gwanatin tarayya Naira Biliyan 6

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta Jamb ta sanar da cewa ta baiwa gwamnatin tarayya kudi shiga da suka kai Naira Biliyan 6 a shekarar 2024.

Kakakin JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Litinin inda yace sun samu jimullar kudin shiga da suka kai Naira N22,996,653,265.25 a shekarar 2024 din.

Yace sun baiwa Gwamnatin tarayya Naira N6,034,605,510.69 daga cikin kudin.

Sanarwar tace kudin da suka baiwa gwamnatin tarayya rara ce da suka samu bayan kammala aikin shirya jarabawar ta shekarar 2024 da cire duk wasu kudade da suka kamata.

Ya kara da cewa a cikin shekaru 7 da suka gabata, sun baiwa Gwamnatin tarayya jimullar kudaden shiga da suka kai naira Biliyan 50.

Karanta Wannan  Kalli hotuna da Bidiyo: Yanda mata suka cire kayansu suka yi zanga-zanga tsirara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *