Wednesday, April 29
Shadow

Gwamnatin Kano na neman a kama Ganduje, saboda yunkurin kafa kungiyar tsaro ta sa kai

Majalisar zartaswar jihar Kano ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike tare da kama tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa wasu kalamai da ta bayyana a matsayin tsokana da kuma tada zaune tsaye kan matsalar tsaro a jihar.

Hakan ya biyo bayan tattaunawa ne a taron majalisar zartarwa karo na 34 da aka gudanar a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar Kano, inda ƴan majalisar suka yi nazari kan kalaman Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin na baya-bayan nan, inda suka yi zargin cewa Kano na kara fuskantar matsalar ƴan fashi da kuma bayyana shirin ɗaukar mutane 12,000 aikin ƴan sandan rundunar tsaro mai suna Khairul Nas.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta kara yawan kudin ciyar da masu laifi a gidan yari inda a yanzu kowanne mutum daya za'a rika ciyar dashi akan Naira 1,125 a kowace rana

Da yake yiwa manema labarai ƙarin haske game da sakamakon taron a ranar Juma’a, kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce kalaman na iya kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da tsaro da gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi.

Majalisar ta ƙara da cewa, ƙasa da sa’o’i 48 bayan an yi waɗannan kalamai, wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kutsa kai cikin wasu al’ummomin kan iyaka a jihar – lamarin da ta ce “ya sanya ayar tambaya kan ko an furta kalaman tare da wata masaniya ce ko kuma suna da alaƙa da harin.”

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda matashi ya tambayi likita wai akwai wata Budurwa a layinsu, yana son tsotsar nonwanta amma tana da cutar Kanjamau, shine yake tambayar shin idan aka tsotsi nonwan me kanjamau ana daukar cutar?

“Ba mu san abin da Ganduje ke nufi da waɗannan kalamai ba saboda haka muna kira da a kama shi, dole ne a bincike shi saboda ba za mu iya kallon sa yana kawo mana cikas a zaman lafiya a jihar ba.” in ji shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *