
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB zata sake shiryawa daliban da suka yi fashi basu samu damar rubuta jarabawar ba.
Shugaban hukumar, ta JAMB Prof. Is-haq Oloyede ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Yace hukumar zata shiryawa kaso 5.6 na daliban da basu samu damar rubuta jarabawar ba.
An dai zargi JAMB din da saka lokaci wanda yayiwa dalibai wahalar iya zuwa wajan jarabawar akan kari.