
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya bayar da labarin cewa, a wasu lokutan jami’an tsaro na kallo wasu abubuwan ke faruwa amma sai su ce wai ba zasu iya daukar mataki ba suna jiran umarni daga sama.
Ya bayyana hakane yayin hira da manema labarai.
Dauda yace wasu lokutan har kuka yake.
Yace abin takaici duk inda wani shugaban ‘yan Bindiga yake a jiharsa ya sani kuma duk inda zasu yana sane amma babu abinda zai iya yi.