Thursday, May 22
Shadow

Jami’ar MAAUN ta rufe gidajen kwanan ɗalibai mata bisa zargin aikata rashin tarbiyya

Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) ta ba da umarnin gaggawa na rufewa tare da janye amincewa da gidajen kwanan dalibai mata na Al-Ansar Indabo da ke Hotoro da titin UDB a birnin Kano.

Wata sanarwa daga Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da Rayuwar Dalibai, Dr. Hamza Garba, a ranar Lahadi, ya bayyana cewa wannan matakin rufe gidajen kwanan wani bangare ne na kokarin da jami’ar ke yi domin tabbatar da kwanan dalibai cikin aminci, tsaro da tsafta, da kuma ci gaba da nuna matsayinta na kin yarda da duk wata dabi’a ta lalata daga kowanne ɗalibi.

“Na samu umarni daga hukumar gudanarwa na rubuta wannan sako don sanar da iyaye da dalibanmu masu daraja cewa jami’a ta janye amincewarta da GIDAJEN KWANAN DALIBAI MATA NA AL-ANSAR INDABO da ke titin UDB da Hotoro,” in ji sanarwar.

Karanta Wannan  Za a sake zaɓar Tinubu a 2027 - Gwamnan Edo

Sanarwar ta kara da cewa, wannan matakin ya zama dole saboda rashin bin ka’idoji da dokokin da jami’a ta shimfida dangane da tafiyar da gidajen kwana na masu zaman kansu.

“Rashin bin ka’idojin ya haifar da wasu abubuwa da ba su dace ba a cikin gidan kwana, kamar aikata alfasha, rashin wadataccen ruwa da wutar lantarki, rigima tsakanin dalibai, yawo ba tare da izini ba a cikin dare, da kuma amfani da kayan more rayuwa tare da wasu mutane da ba a san su ba, wanda ke barazana ga lafiyar dalibanmu.”

“Don haka, an umarci dukkanin daliban da abin ya shafa da su bar gidan kwana nan take bayan kammala jarabawa, kuma su guji ci gaba da zama ko hulɗa da gidajen nan don kare lafiyarku da tsaronku, yayin da hukumar jami’a ke aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cikakken bin wannan umarni,” in ji sanarwar.

Karanta Wannan  Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *