Jami’in ‘Civil Defence’ ya tsinci guzirin wata maniyyaciya a sansanin alhazai na Yola ya kuma mayar mata.

Wani Jami’in hukumar tsaro ta ‘Civil Defence’ mai suna Abubakar Abdulƙadir Mayos, ya mayar da kuɗin guzirin wata maniyyaciya da ya tsinta, har Dalar Amurka $505 da Riyal 30 na Saudiyya a sansanin alhazai na birnin Yolan Jihar Adamawa ya kuma miƙa su ga mai su.
Rahotanni sun baiyana cewa kuɗaɗen mallakar wata maniyyaciya, mai suna Maimuna Salihu Abdullahi, ƴar Jihar Taraba.
Nan take, a cewar rahotanni ya mayar da kuɗin ga jami’an alhazai inda su kuma ba su yi wata-wata ba su ka miƙa mata kayanta a gaban jami’in hukumar NAHCON da daraktan tsare-tsare na hukumar alhazai ta Taraba da sauran jami’ai.