Wednesday, January 15
Shadow

Jam’iyyar Labour ta ce yajin aiki zai ƙara wa ƴan Najeriya wahala ne kawai

Jam’iyyar Labour ta yi kira ga ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya da su sake tattaunawa da gwamnati a kan maganar sabon albashi mafi ƙanƙanta maimakon shiga yajin aiki.

Jam’iyyar ta ce a halin da Najeriya take ciki yajin aiki ba shi da amfani hasali ma zai iya ƙara wa ƴan ƙasar wahalhalun da suke ciki ne.

Babban sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Obiora Ifoh ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

Ya ce tuni daman ƴan Najeriya na fama da katutun matsaloli, a don haka babu buƙatar yin abin da zai ƙara waɗannan wahalhalu.

” Ina ganin neman Naira 494 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ba abu ne mai yuwuwa ba. Abu ne da ba zai ɗore ba saboda hakan na nufin cewa Najeriya za ta ɗauki duk kuɗin da take da shi ta riƙa biyan ma’aikata,” in ji shi.

Karanta Wannan  Hotuna: NLC ta kulle Asibitin Kano

Mista Ifoh ya ƙara da cewa kamata ya yi shugabannin ƙwadagon su ci gaba da tattaunawa da gwamnati a samu matsaya kan abin da zai zama karɓabbe ga ɓangarorin biyu.

Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon na Najeriya na neman gwamnati ta tsayar da Naira 494,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ga ma’aikatan gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba, yayin da gwamnati ke cewa Naira 60,000 za ta amince, abin da ƴan ƙwadagon suka yi watsi da shi.

Rashin cimma matsaya a kan batun a tattaunawar kwamitin musamman na albashin da wakilan ƙungiyoyin ƙwadagon, ranar 28 ga watan da ya wuce, Mayu ya sa ƙungiyoyin tsunduma yajin aikin daga yau Litinin.

Karanta Wannan  APC ta Kano ta yi kira da a kama Kwankwaso

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *