Thursday, May 29
Shadow

Jam’iyyar SDP jam’iyyar karyace kanwar APC ce shiyasa kuka ga ‘yan APC ne kadai ke ta tururuwar shiga cikinta>>Inji Buba Galadima

Babban dan siyasa, Buba Galadima ya bayyana cewa, jam’iyyar SDP kanwar jam’iyyar APC ce, kuma za’a yi amfani da itace dan murkushe ‘yan Adawa.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace idan aka lura yawanci ‘yan APC ne ke komawa cikin jam’iyyar.

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne dai ya fara komawa jam’iyyar SDP wanda daga baya aka samu da yawa suka bishi cikin jam’iyyar.

Karanta Wannan  Kwankwaso ba shi da wani muhimmanci a siyasar Najeriya - PDP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *