
Babban dan siyasa, Buba Galadima ya bayyana cewa, jam’iyyar SDP kanwar jam’iyyar APC ce, kuma za’a yi amfani da itace dan murkushe ‘yan Adawa.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace idan aka lura yawanci ‘yan APC ne ke komawa cikin jam’iyyar.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne dai ya fara komawa jam’iyyar SDP wanda daga baya aka samu da yawa suka bishi cikin jam’iyyar.