Jarumin Finafinan Hausa, Yakubu Muhammad Ya Dauki Nauyin Karatun Wasu Yara Guda Biyu Har Zuwa Jami’a.
Jarumin ya dauki nauyin karatun yaran ne bayan ya ga wani bidiyon su a kafar sadarwa inda suke kalaman aluta da ‘yan jami’a suke yi. Wanda hakan ya sa ya yi tattaki har zuwa garin Wudil domin ganawa da yaran da kuma iyayensu.