
Kocin Algeria, Vladimir Petkovic ya bayyana cewa, Maganar gaskiya Najeriya kawai tafi karfinsu babu wani kamekame.
Yace Najeriya ta cancanci yin nasara a wasan domin ta musu fyadar ‘ya’yan kadanya.
Ya bayyana hakane ga manema labarai bayan Najeriya ta musu 2-0.
Saidai wasu ‘yan Algeria din sun tayar da rikici bayan wasan.