Tsaffin shuwagabannin kasa,Olusegun Obasanjo,Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Abdulsalam Abubakar da Janar Ali Gusau sun yi zama na musamman a kan halin da Najeriya ke ciki.
Sun yi zamanne a gidan tsohon shugaban kasa, IBB dake Minna.
Wata majiya ta bayyana cewa, Rahotannin sun nuna an yi zamanne kan matsalar da Najeriya ke ciki musamman halin matsin tattalin arziki.