
Sanata Natasha Akpoti ta zargi kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da jin haushinta ya hanata ta shiga majalisar a yau saboda ta yi magana game da cin zarafinta.
Ta ce kotu ta soke dakatarwar da aka mata dan haka yanzu tana da ikon shiga majalisar.
Da take magana ga manema labarai a kofar majalisar, Sanata Natasha Akpoti tace ba gaskiya bane cewa wai an dakatar da ita komawa majalisar saboda daukaka kara da majalisar ta yi akan lamarin.
Tace majalisar bata daukaka kara ba kan maganar komawarta majalisar.
Tace hanata shiga majalisar take hakkinta ne dana mutanen mazabarta.
Sanata Natasha Akpoti tace Akpabio ne kakakin majalisar Dattijai mafi muni da aka taba yi.