
Rahoton Marin da mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Jatau yawa Ministan Harkokin kasashen Waje, Yusuf Tuggar na daya daga cikin wadanda suka dauki hankula a yau.
Saidai daga baya Mataimakin gwamnan ta bakin me magana da yawunsa, Muslim Lawal ya musanta hakan.
Amma a wata majiya da muka samo da kafar Sahara Reporters tace tabbas an yi musayar yawu tsakanin Mataimakin gwamnan da Ministan a cikin motar bas data daukesu zuwa fadar Me martaba Sarkin Bauchi.
Rahoton yace ana tsaka da tafiyane sai aka ga fastar Ministan sai gwamna yace zasu yi maganinsa saboda rashin kunyar da yakewa shuwagabannin jam’iyyar jihar.
Saidai Tuggar ya mayar da martanin cewa jihar Bauchi ba kayan kowa bace, hakan yasa mataimakin gwamnan yayi kokarin kaiwa gareshi amma sai jami’an tsaron mataimakin shugaban kasa suka hanashi saboda mataimakin shugaban kasar na zaune tsakaninsu.
Rahoton yace ko da aka tashi komawa, mataimakin gwamnan bai koma a motar bas din data kaisu fadar sarkin ba dan kaucewa kara yin rikici da Ministan.