Friday, December 5
Shadow

Ji Cikakken Bayani kan hadarin jirgin saman Indiya inda mutane sama da 200 suka mùtù, an bayyana kudin diyyar da kamfanin jirgin zai biya iyalan màmàtàn

Wani jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na Air Indiya ya yi hatsari inda ya faɗa kan wata unguwa da ke birnin Ahmedabad a yammacin ƙasar Indiya.

Shugaban kamfanin lura da sufurin jiragen sama na Indiya ya ce akwai fasinjoji da ma’aikata 242 a cikin jirgin.

Bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna baƙin hayaƙi ya turnuƙe bayan rikitowar jirgin.

Babu tabbacin adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata sanadiyyar hatsarin.

Jirgin na kan hanyarsa ne daga Indiya zuwa Birtaniya.

Ma’aikatan kashe gobara da masu bayar da agajin gaggawa sun garzaya wurin da lamarin ya faru.

Akwai yiwuwar dukkanin fasinjojin jirgin Indiya da ya yi hatsari sun mutu

Kamfanin dillancin labaru na AP ya ambato shugaban ƴansanda na birnin Ahmedabad na cewa akwai yiwuwar babu wanda ya tsira da ransa a hatsarin da jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na India Air ya samu yau a birnin.

Karanta Wannan  Ana samun kudi a Najeriya amma yawancin 'yan kasar basa samun kasonsu inda mafi yawa ke cikin bakin Talauci>>Bincike

Ya bayyana hakan ne yayin da bayani ke ƙara fitowa kan hatsarin jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa birnin London na ƙasar Birtaniya.

Jirgin ya faɗa kan wata unguwa jim kadan barin tashi daga filin jirgin Ahmedabad da ke yammacin ƙasar Indiya.

A lokacin da yake jawabi, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin ƙasashen waje ta Najeriya, Randhir Jaiswal ya bayyana hatsarin jirgin a matsayin “babban abin jimami”.

“Ana ci gaba da aikin ceto. Za mu tsaya tukuna domin samun ciakken bayani game da hatsarin,” in ji shi.

Sai dai ya ƙara da cewa: “Mun yi asarar mutane da dama.”

An garzaya da ɗalibai 50 waɗanda jirgi ya rikito musu asibiti

Karanta Wannan  Na yadda da Mukabalar 'yan Izala amma a Turomin Guruntum ko Sheikh Sani Rijiyar Lemu saboda ina son babban dan Izala ne wanda idan na mai Kwaf daya na gama da Izala>>Inji Malam Abdulfatahi Sani Tijjani

Gargaɗi: Akwai bayanai masu tayar da hankali

Ƙungiyar likitoci ta ƙasar Indiya (FAIMA) ta ce an garzaya da ɗalibai masu karatun likitanci 50-60 zuwa asibiti bayan da jirgin Air India da ya yi hatsari ya faɗa kan gidan kwanan ɗaliban.

Ƙungiyar ta kuma ce a yanzu akwai ɗalibai guda biyar da ba a san inda suke ba, yayin da guda biyu kuma an shiga da su ɗakin kula da waɗanda ke cikin matsanancin hali.

Haka nan akwai ƴan’uwan wasu likitocin da su ma ba a san inda suke ba bayan hatsarin.

Ƙungiyar likitocin ta Indiya ta ce yawancin fasinjojin jirgin da aka garzaya da su asibiti an kai su ne a mace.

Karanta Wannan  ƊA ƊUMI-ƊUMI: Amarya A'isha Humaira Da Ango Rarara Sun Sake Sakin Zafafan Hotunan Auransu.

An zaƙulo gawarwaki sama da 200 daga jirgin Indiya da ya yi hatsari

Babban baturen ƴansanda na birnin Ahmedabad da ke ƙasar Indiya ya bayyana cewa an zaƙulo gawar mutane sama da 200 na fasinjojin jirgin Air India da ya yi hatsari a yau Alhamis.

Babban ɗansandan ya fadi hakan ne a matsayin bayani na baya-bayan nan kan hatsarin jirgin, wanda ya rikito ƙasa jim kadan bayan tashi, kan hanyarsa ta zuwa birnin London na Birtaniya.

Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama na Indiya ya ce jirgin na ɗauke ne da mutum 242, kuma akasarinsu Indiyawa ne.

Rahoton yace akwai kananan yara 11 a cikin jirgin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *