Monday, January 19
Shadow

Bayan watanni 3 Dangote ya koma siyo man fetur daga kasar Amurka

Rahotanni sun bayyana cewa matatar man fetur ta Aliko Dangote ta ci gaba da siyo man fetur daga kasar waje bayan kwashe watanni 3 ba tare da yin hakan ba.

Hakan ya fito ne daga jaridar Bloomberg Inda tace yanzu haka akwai jiragen ruwa biyu dauke da man fetur din sun taso daga kasar Amurka zuwa Najeriya matatar ta Dangote.

Hakan na zuwane bayan da aka yi maganar cewa kamfanonin dake hako man fetur a Najeriya zasu rika sayarwa da Dangoten danyen man fetur da kudin Naira maimakon dalar Amurka.

Saidai wannan sabon labari na alamta cewa ga dukkan alamu wannan yarjejeniya ta samu Matsala.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa:Kungiyar dalibai ta kasa, NANS ta nisanta kanta da Comrade Atiku Isa wanda ake zargin dan shugaban kasa, Seyi da wasu manya a kasar nan sun ci zarafinsa tsce ita ba shugabanta bane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *