Friday, December 26
Shadow

Ji Labarin yanda aka yaudari wata matashiyar Najeriya aka kaita kasar Mali da sunan zata yi aiki a Supermarket amma aka ce Qaruwanciy zata yi

Wata matashiyar Najeriya me suna Faith Joseph ta ki amincewa da yin karuwanci bayan da aka yaudareta aka kaita kasar Mali da sunan zata yi aiki a Supermarket.

Matashiyar na aikin gida ne a Afuze, Owan East dake jihar Edo inda aka ce za’a kaita Legas dan ta yi aiki a Supermarket.

Saidai daga baya an tafi da ita kasar Mali, tace sina zuwa aka kaita wajan wata mata wadda Magajiyace, watau uwar Karuwai, data lura da haka sai tace bata yadda ba, ba zata yi ba.

Saidai magajiyar ta gaya mata cewa, aikuwa saidai idan an kawo wata da zata maye gurbinta ne sannan zata iya komawa gida Najeriya.

Karanta Wannan  Ko Dai: Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya gana da 'yan Jam'iyyar PDP, Kalli Hotuna

Matashiya, Faith haka ta zauna har Allah yasa ta lura da wani Ofishin ‘yansanda inda ta tsere zuwa can.

Daga baya dai ta samu an dawo da ita zuwa gida Najeriya.

Shugaban hukumar kula da ‘yan cirani ta jihar Edo, Lucky Agazumah ya tabbatar da faruwar hakan inda yace mutane su rika kawo musu rahoton masu safarar mutane zuwa kasar waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *