Friday, December 5
Shadow

Ji Martanin da Hadiza Gabon tawa wani da yace mata ta bashi kudi

Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta wallafa wannan hoton nata a shafinta na sada zumunta inda masoyanya suka rika yabawa.

Saidai wani ya roketa da ta yiwa mutane kyautar kudi kamar yanda dan siyasa na jihar Kaduna,Bello ElRufai ke yi.

Saidai Hadizar ta mai martanin cewa, ya je ya samu aikin yi.

Ya dai mayar mata da martanin cewa, ko ya kawo takardunsa ta bashi aiki a dakin hada shirye-shiryenta na Youtube?

Daga nan dai Hadizar bata sake takashi ba.

A baya dai, Abokiyar aikin Hadizar, Rahama Sadau ta rabawa masoyanta kudade ta shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya kara aure, 'Yar Kannywood ce ya aura, Ji bayani game da fina-finan da ta yi da sanda aka daura auren

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *