
Mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore sannan dan fafutuka ya bayyana cewa, X sub aika masa da sako cewa, Gwamnatin Najeriya ta nemi a kulle masa shafi.
Sannan ya goge rubutun da yayi akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Shi dai Sowore ya rubuta cewa “wannan me laifin, Tinubu ya je kasar Brazil ya ce ya magance matsalar rashawa da cin hanci amma hakan ba gaskiya bane”
DSS sun ce wannan bayani na Sowore labarin karyane sannan yana barazana ga tsaron Najeriya hakanan kuma ya batawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna a idon Duniya, dan haka suka nemi X ta kulle shafin Sowore nan da awanni 24 ko kuma a dauki mataki akanta.
Saidai Sowore yace ba zai goge wannan rubutu da yayi ba.