Dan Tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai ya yi shagube ga gwamnan Kaduna na yanzu,Malam Sanata Uba Sani a shafinsa na Twitter.
Dama dai tuni baraka ta kunno kai tsakanin Gwamna Uba Sani da Malam Nasiru El-Rufai.
An wallafa wani bayani dake cewa, Jihohi kalilan ne suka jawo zuba hannun Jari a gaba daya Najeriya kuma babu jihar Arewa ko daya a cikinsu.
A martanin dan tsohon Gwamnan, sai cewa Yayi:
G-Fresh ya kashe Naira Biliyan 3 wajan tafiye-tafiye tun bayan da ya shiga ofis.
Duk da yake bai kama suna ba, da yawa dai sun yi amannar da Gwamna Malam Uba Sani yake.