Thursday, January 15
Shadow

Ji sunayen Gwamnoni 5 da zasu koma APC saboda goyon bayan sake zaben shugaba Tinubu a 2027

Jam’iyyar APC tace akwai karin Gwamnoni 5 da zasu koma jam’iyyar nan da watanni 2.

Mataimakin shugaban jam’iyyar daga yankin kudu maso gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi a jaridar Punchng.

Ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Bayelsa, Rivers, Plateau, Kano, da daya daga cikin gwamnonin Abia ko na Enugu ne zasu koma jam’iyyar APC.

Yace wannan ba jita-jita bane, tabbas ne kuma nan da watanni 2 kowa zai tabbatar da hakan.

Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC inda yace zai je ya kula da lafiyarsa.

Karanta Wannan  Kalli 'Yar shekara 30 na kukan rashin miji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *