Yadda Gwamna Abba Gida-gida ya taimaki dalibar da ke fama da lalura bayan ta tura masa sako na neman taimako.

A cikin wani lamari mai ratsa zuciya , wata mata mai karfin gwiwa da buri, Mai suna Ummi mai shekaru 31, ta samu kulawar da ta daɗe tana mafarki daga gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Ummi ta shafe kusan shekaru 18 tana fama da wata cuta mai suna Proximal Myopathy, wadda ke sa raunin tsokokin jiki. Duk da wannan ƙalubale, ta kammala karatunta a fannin shari’a, amma rashin lafiya ya hana ta zuwa makarantar koyon aikin lauya (Law School).
Duk da rashin tabbacin amsa, Ummi ta aike da saƙon neman agaji ga Gwamna Abba Kabir Yusuf. Cikin abin mamaki da tausayawa, Gwamna ya karanta saƙon kuma ya ɗauki matakin gaggawa. Wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda Gwamna ya gana da Ummi kai tsaye, tare da nuna jajircewa wajen taimaka mata.
A cewar Gwamna, ya umurci jami’ansa da su binciki lamarin Ummi da kyau. Bayan gwaje-gwaje, Gwamna ya ɗauki nauyin duk wata kulawar lafiya da take bukata, ciki har da magunguna, kayan jinya da na’urorin taimako masu tsada da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
An ba Ummi kujerar tafiya da ƙafa (wheelchair), kayan kula da lafiya, da sauran na’urori masu taimakawa wajen sauƙaƙe rayuwarta. Daga cikin abubuwan da suka fi kayatarwa, Gwamna Abba ya riƙe hannunta ya ce: “Daga yau, ke ‘Ya ta ce. Duk abinda kike bukata, ki turo min saƙo kai tsaye.” Haka kuma, ya haɗa ta da ƴarsa ta cikinsa wadda itama dalibar lauya ce domin taimaka mata a fannin karatu.
Gwamna Abba ya ƙara da bayar da kayayyakin abinci masu yawa, sannan ya ɗauki Amina – mai kula da Ummi – aiki a gidan gwamnatin Kano. Ya kuma tabbatar musu da cewa za su gudanar da Sallah babba cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, tare da basu kyaututtuka masu yawa.
Da hawaye a idonta, Ummi ta bayyana farin cikinta da godiya ga wannan karamci da aka nuna mata.