
Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana wani ɗan gidan yari, Bright Ngene na jam’iyyar Labour da aka ɗaure saboda satar naira miliyan 15, a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Enugu ta kudu da aka yi a ƙarshen makon da ya gabata.
Mai magana da yawun hukumar a jihar, Sam Olumekun ya gabatar da sakamakon, bayan soke wanda aka yi a 2023.
RFI ya rawaito cewa a ranar 28 ga watan Yulin wannan shekara alkali ya ɗaure Ngene shekaru 7 a gidan yari, saboda samun sa da laifin satar naira miliyan 15 kuɗaɗen al’ummar yankin da ya fito da ke Jihar Enugu.
Rahotanni sun ce ya aikata laifin ne tun a shekarar 2017, amma a lokacin alkali ya bada damar cewar a kai shari’ar hukumar sasanta al’umma.
Amma bayan nasarar da ya samu a zaɓen shekarar 2023, sai alkalin ya ce an ba shi umarnin ci gaba da gudanar da shari’ar, inda cikin ƙanƙanin lokaci aka gudanar tare da yanke hukunci.
Yayin gudanar da zaben cike gurbin da aka yi a ƙarshen mako, jam’iyyar Labour bata sauya sunan sa ba, saboda haka sunan sa ne a cikin jerin ƴan takarar da aka gabatar, abinda ya ba shi damar samun nasara.