
Mafusatan matasa sun bankawa wani mutum me suna Egholor wuta ya mutu bayan da aka zargeshi da kashe wata dattijuwa.
Lanarin ya farune a Ukpiovwin community, Udu dake jihar Delta kuma rahotanni sunce rikicin fili ne ya hadasu.
Matar dai ta tafi gonane amma har magariba ta yi bata dawo ba.
da ‘ya’yanta suka ga haka shine suka vi sahu, suna zuwa sai suka tarar da gangar jikinta an yanke mata kai. Anan suka harzuka suka bazama neman wanda yayi wannan aika-aika.
Daya daga cikin ‘ya’yan nata ya bayyana cewa, ya tuna akwai wani mutum da suka yi rikicin fili dashi kuma har yayi barazanar kasheta.
Nan suka tunkari gidan mutumin i da suka zameshi, da ya ji tuhuma ya amsa laifinsa, inda nan take aka bankawa gidansa wuta har shi ya kone.
An yi kokarin jin ta bakin kakakin ‘yansandan jihar, Bright Edafe amma bai amsa kiran shi da aka ta yi ba.