Friday, July 17
Shadow

Daya daga cikin ‘yan majalisar Amurka da ke Zuga Trump akan Najeriya na shan suka bayan da yace Garin da aka yi Gharkuwa da ‘yan mata ‘yan Makaranta a jihar Kebbi garin Kiristane

Dan majalisar Amurka, Riley M. More dake zuga shugaban kasar Amurka, Donald Trump akan Najeriya yace ‘yan mata ‘yan makaranta da aka yi garkuwa dasu a jihar Kebbi garin Kirista ne.

Hakan ya jawo masa suka da Allah wadai.

Daya daga cikin wadanda suka mayar masa da martani, akwai tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad inda yace garin da aka sace daliban ba garin Kirista bane, garin musulmi ne kuma daliban ma musulmai ne.

Kasar Amurka dai ta sha Alwashin kawo hari dan tallafawa Kiristocin Najeriya bisa zargin cewa, ana musu Khisan Khiyashi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Shugaba Tinubu bai shiga cikin garin Jos ba, A filin jirgin da ya sauka aka kai jama'ar da lamarin ya rutsa dasu ya gana dasu, lamarin ya jawo cece-kuce sosai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *