
Hukumomin kula da iyaka na kasar Ingila sun kama wasu mutane biyu mace da namiji daga Najeriya wanda suka yi yunkurin shiga kasar da wani yaro da aka yi amannar satoshi suka yi.
Hukumomin kula da iyakar a filin jirgin sama na Manchester sun tsargu da mutanen bayan ganin yanda suke tafiya da yaron.
Ko da aka bincikesu sai namijin me suna Raphael Ossai yace shine mahaifin yaron sannan kuma matar da suke tare Oluwakemi Olasanoye wai itace mahaifiyar yaron.
Saidai da bincike yayi tsanani, an gano cewa, akwai kuma wata takardar haihuwa data bayyana wata mata dake zaune a kasar ta Ingila wadda aka bayyana da cewa itace mahaifiyar yaron.
Tuni dai aka kama matar da namijin.