Monday, March 24
Shadow

Ji yanda Dansandan Najeriya ya bide wuta a ofishin ‘yansandan ya ķķàshè mutum daya ya kuma jikkata wasu

Dansandan Najeriya me suna Effiong Bassey ya bude wuta a Ofishin da yake aiki na Atakpa Divisional Police dake jihar Cross Rivers inda ya kashe wata mata daya sannan ya jikkata wasu mutane 2.

Lamarin ya farune da dukudukun ranar Lahadi bayan da Effiong ya koma ofis bayan ya kammala aikin dare a bankin Ekondo Microfinance Bank.

Kakakin ‘yansandan jihar, Ugbo Irene ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace Effiong ya nuna rashin da’a inda aka bukaci ya bayar da bindigarsa ta AK47 amma yaki.

Yace ya tare kofar shiga ofishin inda ya hana shiga ko fita kamin daga baya ya bude wuta.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka gurfanar a kotu kan zanga-zanga

Yace cikin mutane masu wucewa da ya harba hadda wata mata me suna Ijeoma Wilson Obot ‘yar kimanin shekaru 41 da haihuwa wadda ta rasu, sauran 2 kuma suka jikkata.

Yace tuni kwararrun ‘yansanda suka je wajen inda suka kwace bindigar dake hannun dansandan sannan aka kamashi.

Yace wanda suka jikkata suna asibiti, sannan AIG na Zone 6 da tawagar kwamishinan ‘yansanda na jihar Rivers sun kaiwa wanda suka jikkata ziyara a Asibiti inda har ya bada kudin kula dasu sannan ya bayar da tabbacin za’a yi adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *