Wednesday, January 14
Shadow

Ji yanda jami’an tsaro suka kama abubuwan fashewa a garin Daura dake jihar Katsina

Rahotanni daga garin Daura na jihar Katsina sun bayyana cewa, hukumomi sun kama wata motar Golf dauke da ababen fashewa.

Lamarin ya farune ranar 7 ga watan Janairu.

Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Abubakar Aliyu ya tabbatar da hakan inda yace sun kama Direban motar me suna Jamilu Musa dan shekaru 40.

Yace an bashi kayan ne daga Kano zuwa Kongolom.

Bayan da bincike ya tsananta, an sake kama karin wasu mutane 2, Ibrahim Murtala da Sulaiman Muhammad.

Hukumomin ‘yansandan sun bayyana cewa, za’a gurfanar dasu a gaban kotu.

Karanta Wannan  Matan Yarbawa sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin samar masa da kuri'u Miliyan 1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *