
Wannan matashiyar me suna Jennifer ta fuskanci hukuncin daurin shekaru 7 ko biyan tarar Naira 450 bayan da kotu ta sameta da laifin zamba da bata lokaci.
Wani mutum ne me suna Emmanuel ne da suka hadu a kafar sada sumunta ya aika mata da Naira dubu 150 dan ta sameshi a Abuja.
Saidai ta cinye kudin kuma ta ki zuwa ta biya masa bukata.
Dalilin hakane ya kaita kotu.
Kotu dai ta sameta da laifin zamba da bata lokaci dan haka aka yanke mata hukuncin Daurin shekaru 7 a gidan yari ko biyan tarar Naira dubu. 450