
Lauya me rajin kare hakkin bil’adama, Festus Ogun ya maka gwamnan jihar Legas, Babajide Sonwo Olu a kotu saboda ya yi blocking dinsa a X.
Lauyan ya gabatar da karanne a babbar kotun tarayya dake Legas.
Ya nemi kotu tasa Gwamnan Legas ya cire Blocking din da yayi masa saboda hakan take hakkinsa ne a matsayinsa na zababben gwamna wanda aka zaba a turbar Dimokradiyya.
Ya kuma nemi kotun data sanya Gwamnan Legas ya bashi hakuri.