
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kaiwa sojojin Najeriya na rundunar Operation FANSAR YAMMA dake yaki da ‘yan Bindiga a jihar Katsina ziyarar ba zata dan ya ga yanda ake gudanar da aiki.
Shugaban ya je ne ba tare da jami’an tsaronsa ba kamar yanda aka saba.
Ya karfafa sojojin musamman yanda suka sadaukar da rayuwarsu dan samarwa mutanen Najeriya tsaro.
Yace zasu yi kokarin biyan sojojin dukkanin hakkokinsu da kuma inganta rayuwarsu data iyalinsu.