Friday, December 5
Shadow

Ji Yanda ‘Shugaban ‘yansandan Najeriya ya karawa Dogariyarsa mace mukami ba tare da ta rubuta jarabawar karin mukamin ba’

Ana zargin shugaban ‘yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun da karawa dogariyarsa mace,Yemisi Ademosu mukami ba tare da ta rubuta jarabawar karin mukamin ba.

Rahoton yace An kara mata mukami daga ASP ne zuwa DSP.

Wasu majiya daga hukumar ‘yansandan ne suka bayyanawa kafar Sahara reporters kamar yanda suka ruwaito.

Rahoton yace dama Yemisi Ademosu ta fara aikin ‘yarsanda ne a matsayin dogariyar shugaban ‘yansandan kuma yanzu duk inda zashi suna tare a fadin Najeriya.

Rahotan yace tun bayan da aka baiwa Kayode Egbetokun mukamin shugaban ‘yansandan Najeriya, Yemisi ya koma zama a Abuja gaba daya.

Hakana bayan Yemisi, akwai kuma Bukola Kuti da itama, Sahara reporters ta ruwaito cewa na da alaka ta kut da kut da shugaban ‘yansandan wadda itama dogariyarsa ce.

Karanta Wannan  TURKASHI: Wani Matashi da ya Sadaukar da ransa da rayuwarsa ga, Sen. Barau I jibrin

A cewar Rahoton itama tana samun ci gaba sosai a hukumar ‘yansanda wanda bata cancanci samu ba.

Rahotan na zuwane a yayin da ‘yansanda da yawa ke neman a musu karin mukami bayan da suka cika duk wasu sharudai da suka kamata amma ba’a musu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *