Saturday, November 8
Shadow

Lauya ya baiwa NBC wa’adin kwanaki 30 da ta soke ko kuma hana bàtssà a shirin BB9ja

Lauya ya baiwa NBC wa’adin kwanaki 30 da ta soke ko kuma hana batsa a shirin BB9ja

Wani lauya mai rajin tabbatar da gaskiya, Maduabuchi Idam, ya rubuta takardar korafi ga Darakta Janar na Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Kasa (NBC), yana bukatar a dakatar da shirin talabijin na gasar Big Brother Naija.

Idam ya ce ya kamata a soke ko kuma a daidaita sahun shirin saboda ya na tallata abubuwan batsa, rashin kunya, da kalaman da ba su dace ba, wanda hakan ya saɓa da dokar NBC ta 1999.

Ya bayyana cewa shirin, wanda ke cikin mako na biyu a halin yanzu, ya kasance cike da nuna ayyuka na batsa da lalata a fili da kuma a lokacin da shirin ke gudana kai tsaye.

Karanta Wannan  Obasanjo Ya Ziyarci Uwargidan Shugaban Kasa Bayan 'Yan Kwanaki An Hange Shi Sanye Da Hula Kalar Tambarin Tinubu

“Ina cikin bacin rai matuka da ganin cewa ba wai kawai ana watsa shirin a talabijin na kasa ba, har ma ana yada abubuwan batsa da rashin kunya daga shirin a shafukan sada zumunta na kamfanin da ke daukar nauyin shirin, ba tare da la’akari da tarbiyya da mutuncin jama’a ba.”

Ibam ya buƙaci NBC da ta sa ido ko ta daidaita shirin BBNaija, yana mai cewa bai kawo wata fa’ida ta ilimi, fasaha, kimiyya, ko adabi ga al’umma ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *