Yadda Na Yi Ido Biyu Da Wanda Suka Yi Garkuwa Da Ni A Masallaci, inji Cmr. Mb Muhammad.

“Na yi alwala zan yi Sallah a gidan man Shema dake Bakin Ruwa Kaduna, sai na ga daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da ni a masallacin shi ma zai yi sallah.
Bayan mun idar a Salla sai na tambaye shi ka gane ni? Yace eh ya gane ni, amma yanzu amma yanzu na tuba na daina wannan mummunar harkar ta ta’aďdancin, yanzu haka ma sana’ar acaba nake yi don na rufawa kaina da iyalina asiri. Sauran abokanan sana’ar mu wasu an kashe su wasu kuma sun tuba inji shi dan ta’aďdan, daga karshe na ce na yafe masa kuma na yi masa alkairi”.
Shin idan kai ne za ka yafe masa?
Daga Madubi H