Tuesday, May 19
Shadow

Ji yanda ta kaya bayan da Na Yi Ido Biyu Da Wanda Suka Yi Gàrkùwà Da Ni A Masallacin garin mu, inji Cmr. Mb Muhammad

Yadda Na Yi Ido Biyu Da Wanda Suka Yi Garkuwa Da Ni A Masallaci, inji Cmr. Mb Muhammad.

“Na yi alwala zan yi Sallah a gidan man Shema dake Bakin Ruwa Kaduna, sai na ga daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da ni a masallacin shi ma zai yi sallah.

Bayan mun idar a Salla sai na tambaye shi ka gane ni? Yace eh ya gane ni, amma yanzu amma yanzu na tuba na daina wannan mummunar harkar ta ta’aďdancin, yanzu haka ma sana’ar acaba nake yi don na rufawa kaina da iyalina asiri. Sauran abokanan sana’ar mu wasu an kashe su wasu kuma sun tuba inji shi dan ta’aďdan, daga karshe na ce na yafe masa kuma na yi masa alkairi”.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon Wani barawo da aka kama: Ya shiga gidan da ake gini ya saci Sabbin Bokitan fenti 60 da darajarsu ta kai Naira Miliyan 1.5, ya tsiyaye fentin ya sayar da kowane bokiti Naira Dubu daya

Shin idan kai ne za ka yafe masa?

Daga Madubi H

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *