
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayar da labarin cewa, akwai sanda ya tuka mota daga kaduna zuwa Abuja yana bacci inda yace allah ne ya tuka motar ya kaisu Abuja lafiya.
Ya ce a lokacin sun je Kanone sun nada sarki, zasu koma sai aka hana sayar musu da tikitin jirgin sama.
Yace sai ya kira tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar dashi inda Kwankwason yace masa ya je gidan gwamnatin jihar.
Saidai yace a yayin da yake shirin tafiyane sai shugabab DSS na Kano ya sameshi yace masa duk abinda yake ciki ya fice daga garin Kano dan ba zai iya bashi tabbacin kariyar rayuwarsa ba.
Yace ya gayawa shugaban DSS din yanda suka yi da Gwamna, yace masa amma kada ya sake ya je gidan gwamnatin, su fice daga Kano kawai.
Amachi yace tare dashi akwai Goje, Baraje da Professor Gambari, yace haka suka samu mota suka zuba mai suka kama hanyar zuwa Kaduna.
Yace duk ukun bacci ya kwashesu sai shi kadai yana ta tuki.
Yace da suka je Zaria ya sauka ya sayi lemun Red Bull guda 6 saboda ya fara jin bacci shima amma duk da haka basu hanashi bacci ba.
Yace haka yayi ta bacci yana tuki, Allah ne ya tuka motar daga Kaduna zuwa Abuja ya kaisu Lafiya.