
Rundunar ƴansanda a jihar Jigawa sun ce sun kama wani mutum bisa zargin kashe matar ƙaninsa a ƙauyen Gunka da ke karamar hukumar Jahun a jihar.
Wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar SP Lawan Shiisu Adam ya fitar ranar Alhamis, ya ce ana zargin mutumin mai suna Buhari Sule mai shekara 25 da far wa matar ƙanin nasa – inda ya lakaɗa mata shegen duka har ta kai ga mutuwarta.
Sai dai ya ce ana tunanin cewa ba shi da lafiyar kwakwalwa, saboda baya ga kashe matar, ya kuma raunata ɗiyar makwabciyarsa ta hanyar yi mata duka da taɓarya.
Sanarwar ƴansandan ta ce lamarin ya faru ne ne ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu da misalin karfe 5:30 na yamma a ƙauyen na Gunka.
“Bayan da muka je wurin da lamarin ya faru ne muka garzaya da waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Jahun domin yi musu magani. Sai dai ɗaya daga cikinsu ta mutu a asibitin yayin da ɗayar kuma ke samun kulawa,” in ji Shiisu Adam.
Ya ce wanda ake zargin yana hannunsu a yanzu kuma suna ci gaba da bincike.