
Wani abin ban mamaki da ya faru shine yanda aka gano wasu bata gari dakewa kananan yara maza wayau suna aika musu hotunansu tsirara.
Yaran dai nantsakanin shekaru 14 zuwa 21 ne.
Wasu daga cikinsu da saninsu ake aikata hakan saboda ana basu kudi, wasu kuma ba da saninsu ba saboda an musu wayau ne.
Jaridar Punchng ta yi bincike akan lamarin kuma ta gano cewa ana amfani da kafafen sada zumunta ne irin su X ne wajan aikata wannan masha’a.
Saidai ana ta kulle irin wadannan shafuka amma masu aikata wannan masha’a sai su kara bude wasu.
Wasu yaran da a yanzu sun girma amma ana da Bidiyonsu suna cikin fargaba saboda a yanzu ana ta yada Bidiyon a kakafen sada zumunta wanda hakan yana zamar musu Abin Kunya.
An yi kira ga gwamnati, da ta dauki matakai kan lamarin dan tsafta kafafen sada zumunta irin su Facebook, Twitter, da Telegram.