Thursday, May 8
Shadow

Ji yanda ‘yansanda suka kama wani matashi da ya Kàshè mahaifinsa yayi gunduwa-gunduwa da gawarsa

‘Yansanda a jihar Legas sun kama matashi dan kimanin shekaru 24 me suna Sowe Temidayo Igbekele bisa zargin kashe mahaifinsa, Babatunde Sowe Kayode da shekaru 60 a Unguwar Oshodi.

An kama matashinne ranar Lahadi bayan wata ‘yar uwarsu me suna Temidayo Akinola ta kai korafi ofishin ‘yansandan.

Lamarin ya farune ranar 17 ga watan Afrilu da misalin karfe 9:00 a.m. zuwa yanzu dai ba’a san dalilin dan na aikata abinda ya aikata ba.

Tuni ‘yansandan suka je suka tattara gawar mahaifin aka tafi bincike.

Matashin da ya tsere bayan aikata wannan laifi an bi sahunsa an kamashi.

Karanta Wannan  Hotuna YANZU-YANZU: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Taho Da Yaran Jihar Kano Zuwa Gida Yanzu Haka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *