
Rahotanni sun bayyana cewa, Habu Dan Damisa da aka kashe ya mutu ne a hannun ‘yansanda.
Habu Dan Damisa sanannen dan daba ne dake kashe mutane da yi musu zalinci kala-kala amma saboda ana ganin yana da daurin gindi a wajan wasu ‘yan siyasa yasa yaki tabuwa.
Mutuwarsa ta zowa mutane da yawa da mamaki musamman jin cewa, a hannun ‘yansandan ya mutu.
Rahotanni sunce an yi kokarin hana ‘yansanda kashe Dan Damisa amma suka ki sauraren wannan kiraye-kirayen musamman la’akari da irin barnar da yake yi a cikin al’umma suka aikashi lahira.