Wednesday, January 15
Shadow

Jihar Gombe ta kulla yarjejeniya da kamfanin kasar China dan samarwa da kanta wutar Lantarki

Gwamnatin jihar Gombe ta samarwa da kanta hanyar samun wutar lantarki wadda ba sai ta dogara da gwamnatin tarayya ba.

Gwamnatin ta sakawa wata yarjejeniyar samar da wutar me karfin megawatt 100 daga hasken Rana hannu tare da kamfanin China18th Engineering na kasar China.

Gwamnan jihar Inuwa Yahya ya bayyana cewa, hakan zai basu damar karfafa huldar kasuwanci a jihar.

Yace kudirin dokar da majalisa ta yi da ya baiwa jihohi damar samarwa da kansu wutar lantarki da rabata ne ya basu damar kaiwa ga wannan mataki.

Karanta Wannan  Wahalar rayuwa tasa yanzu matasan Najeriya na zuwa kasar Nijar neman aiki>>Jafar Jafar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *